1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin rage karfin Amirka a tsaron Turai

November 10, 2018

Shugaban kasar Faransa Emanuel Macron ya bayyana cewa kamata ya yi kasashen Turai su tashi haikan dan tsaron kasashensu maimakon dogaro da kasar Amirka kadai.

https://p.dw.com/p/3818w
Paris US-Präsident Trump und Macron
Hoto: Reuters/C.P. Tesson

 Shehuba Marcon wanda ke karban bakoncin shugabannin kasashen wadanda ke hallartan bikin zaman lafiya wanda ke gudanan a wani bangaren bikin cikar shekaru 100 da kawo karshen yakin duniya na daya, ya nuna cewa dogaro da Amirka ba mafita ba ce. Tun a jajiberin ganawarsu da Donald Trump ne dai, Emanuel Macron ya fada wa wata kafar yada labarai cewa, akwai bukatar kasashen Turai su kafa rundunar sojansu ta daban wanda babu hannun Amirka a ciki. Shi kuwa a nasa martanin Trump yace fadin hakan tamkar izgilanci ne ga Amirka. Shugabannin kasashen duniya da yawa ne ke hallalatar bikin wanda ke gudanan a birnin Paris.