1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Qatar ta buƙaci tura sojoji domin shawo kan rikicin Siriya

September 25, 2012

Daular Qatar ta nemi tura dakarun ƙasashen Larabawa zuwa Siriya, tunda a cewar ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta gaza warware rikicin.

https://p.dw.com/p/16EWU
Egypt's President Mohamed Mursi talks at the Arab League headquarters in Cairo September 5, 2012. Mursi, promising to put Cairo back at the heart of Arab affairs, made an impassioned appeal to Arab states on Wednesday to work for an end to the bloodshed in Syria and said the time had come to change the Syrian government. REUTERS/Egyptian Presidency/Handout (EGYPT - Tags: POLITICS) FOR EDITORIAL USE ONLY. NOT FOR SALE FOR MARKETING OR ADVERTISING CAMPAIGNS. THIS IMAGE HAS BEEN SUPPLIED BY A THIRD PARTY. IT IS DISTRIBUTED, EXACTLY AS RECEIVED BY REUTERS, AS A SERVICE TO CLIENTS
Hoto: Reuters

Sarkin daular Qatar ya buƙaci tura dakarun ƙasashen Larabawa domin shiga tsakani a rikicin da ke ci gaba da wanzuwa a ƙasar Siriya da nufin shawo kan rikicin. Sheikh Hamad bin Khalifa Al-Thani, da ke zama jigo wajen nuna goyon baya ga 'yan adawar Siriya ya gabatar da wannan buƙatar ce ga babban taron Majalisar Ɗinkin Duniya da ke ci gaba da gudana a birnin New York na ƙasar Amirka, bayan da babban sakataren Majalisar, Ban Ki Moon ya kwatanta rikicin na Siriya da cewar wata Annoba ce da ke yin barazana ga zaman lafiyar duniya baki ɗaya.

Shi kuwa shugaban Amirka Barak Obama kira ne ya yiwa al'ummomin ƙasa da ƙasa da su haɗa hannu da hannaye wajen fafutukar kawo ƙarshen mulkin shugaba Bashar al-Assad na ƙasar ta Siriya.

A cewar sarkin na daular Qatar, tunda al'ummomin ƙasa da ƙasa sun gaza kawo ƙarshen rikicin na Siriya, to kamata yayi ƙasashen Larabawa su yi gaban kansu wajen shiga tsakani bisa dogaro da dalilai na jin ƙan bil'Adama dana siyasa da kuma na soji wajen yin abinda ya dace da nufin kawo ƙarshen zubar da jinin da ke afkuwa a ƙasar.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou