1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Koriya ta Arewa: Trump ya saba alkawari

Abdul-raheem Hassan
May 25, 2018

Duk da soke alkawarin ganawa tsakani shugabannin Koriya ta Arewa da Amirka ta yi, gwamnatin Pyongyang ta ce kofa a bude take domin tattaunawa a kowani lokaci.

https://p.dw.com/p/2yIN3
Südkorea TV Bildschirm Donald Trump, Kim Jong Un
Hoto: picture-alliance/AP Images/A. Young-joon

Ma'aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ta ce matakin da shugaba Donald Trump ya dauka na soke ganawar karya alkawari ne, kuma bai cimma burin sauran kasashen duniya ba. Amma dai gwamnatin Pyongyang a shirye ta ke a ko wani lokaci domin sake shiga tattaunawar. Trump ya ce matakin da ya dauka ya biyo bayan martanin Koriya ta Arewa kan kalaman matakin da Amirka za ta iya dauka kan Koriya ta Arewa idan ta ci gaba da cijewa kan sarrafa makaman nukiliya, Trump ya ce soke haduwar shi ne matakin da yafi dacewa da kasashen biyu. Soke ganawar dai na zuwa ne jim kadan bayan da Koriya ta Arewa ta sanar da rusa cibiyar gwajin makaman nukiliyarta, sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana takaicin rashin cika alkawarin ganawa shugabannin biyu da aka dade ana jira.