1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ci gaba da katse makamashin gas

Binta Aliyu Zurmi
July 20, 2022

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya dora alhakin janyewar makamashin gas dinsa a kan kasashen yamma, ya kuma yi gargadin cewar makamashin ka iya ci gaba da kafewa.

https://p.dw.com/p/4EO74
Iran Russland Türkei | Dreiergipfel | Wladimir Putin, Ebrahim Raisi und Recep Tayyip Erdogan
Hoto: Sergei Savostyanov/TASS/dpa/picture alliance

Wadannan kalaman na mahukuntan Moscow dai ya kara tabbatar wa kasashen Turai da zulumin da suke yi na yiwuwar ya katse makamashin da kasashe da dama ke dogaro da shi.

Matakin da ya jefa su cikin rudani da ma kiran taron gaggawa da zai gudana a gaba a yau don daukar matakan da suka kamata, musamman na takaita amfani da makamashin da kasashen ke da a yanzu haka domin zama a cikin shirin ko ta kwana da wanda a nan gaba za a shiga lokacin hunturu da ake da matukar bukatar makamashin.

Dama dai an jima ana zargin Putin ka iya daukar wannan mataki a matsayin ramuwar gayya ga takunkuman da kasashen Turai suka kakaba masa tun bayan kaddamar da mamayar da yayi a kasar Ukraine.