1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin na ziyarar rangadi a Vietnam

Abdullahi Tanko Bala
June 20, 2024

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya fara wata ziyarar rangadi a Vietnam kwana guda bayan kulla yarjejeniyar tsaro da shugaban Koriya ta arewa Kim Jong Un.

https://p.dw.com/p/4hHWl
Vladimir Putin na ziyara a Vietnam
Vladimir Putin na ziyara a VietnamHoto: Minh Hoang/AP Photo/picture alliance

Putin da Kim sun rattaba a kan yarjejeniyar mai muhimmanci a taron kolin da suka yi a birnin Pyongyang da ta hada da alkawarin kai wa juna dauki idan an kai musu hari.

Kim ya kuma jaddada cikakken goyon bayansa ga Rasha a yakin da ta ke yi da Ukraine.

Amurka da kawayenta sun zargi Koriya ta arewa da bai wa Rasha makamai a yakin Ukraine, yayin da yarjejeniyar da suka kulla ta fara haifar da fargabar cewa za ta bai wa Rasha karin makamai.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta ce kara karfafa dangantaka tsakanin Rasha da Koriya ta Arewa abin damuwa ne kwarai inda a waje guda wani babban jami'in diflomasiyyar Ukraine ya zargi Koriya ta Arewa da mara wa Rasha baya wajen aikata kisan kare dangi.

Kasashen biyu dai sun kasance aminan juna tun kafuwar Koriya ta arewa bayan yakin duniya na biyu.