1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin na neman mutunta Kirsimeti Orthodox

Mouhamadou Awal Balarabe
January 5, 2023

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya umurci sojojin kasarsa da su tsagaita bude wuta na sa'o'i 36 a Ukraine don mutunta bikin Kirsimeti na darikar Orthodox da zai gudana a karshen mako.

https://p.dw.com/p/4LnTO
Russland Patriarch Kyrill und Wladimir Putin
Hoto: Mikhael Klimentyev/AFP/Getty Images

Wannan umurnin ya biyo bayan shawarar da shugaban darikar cocin Orthodox na Rasha Patriarch Kirill ya gabatar na bai wa al'ummar Ukraine damar halatar adu'o'i a coci. Amma wani mai ba da shawara ga shugaban kasar Ukraine, Mykhailo Podoliak, ya danganta matakin tsagaita wuta na Rasha da "munafunci", yana mai kira ga sojojin Moscow da su tattara nasu ya nasu su bar yankunan da suka mamaye.

Dama shi ma shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi irin wannan kira, inda ya bukaci takwaransa na Rasha Vladimir Putin da ya tsagaita bude wuta a kasar Ukraine, tare da zama kan teburin sulhu domin gano bakin zare warware rikicin. Sai dai Ukraine ta bukaci Rasha ta janye daga yankunan da ta mamaye kafin ta zauna kan teburi guda da ita.