1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Putin na neman hanyar waware rikicin Iran

Mouhamadou Awal Balarabe
August 14, 2020

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya ba da shawarar shirya taron koli na manyan kasashen duniya ciki har da Jamus don neman warware takaddamar nukiliyar Iran bayan da Amirka ta fita daga yarjejeniyar.

https://p.dw.com/p/3gzhb
Iran Teheran Syrien Gipfel - Putin trifft Rohani
Hoto: picture-alliance/TASS/M. Metzel

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya bukaci da a gudanar da taron koli na kasashe masu kujerar dindindin a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da kuma Jamus da Iran, don gano bakin zaren warware takaddamar nukiliyar Iran. Wannan sanarwar ta zo ne a yayin da Amirka ta kuduri aniyar tsawaita takunkumin kan cinikin makamai da Teheran, wanda ya kamata ya kare a ranar 18 ga Oktoba. Sai dai Rasha ta ki ba da kai a kan wannan batu saboda a cewar ta, zai maida hannu agogo baya a kokarin sulhunta rikicin na Iran.

Shugaban na Rasha ya ce lokaci ya yi da za a nemi kauce wa duk wani rikici da zai ci gaba da jefa tattalin arzikin Iran cikin mawuyacin hali. Kasar Amirka wacce ta janye daga yarjejeniyar nikiliyar Iran a watan Mayun 2018, tana neman ci gaba da ja wa Iran birki a fannin siyan makamai. Sai dai  kasashen China da Rasha, wadanda ke da kujerar na ki a kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya suna adawa da matakain tsawaita wannan takunkumin.