1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaIndonesiya

Prabowo Subianto zai dauki madafun ikon Indonesiya

Suleiman Babayo USU
April 24, 2024

Hukumar zaben Indonesiya ta tabbatar da Prabowo Subianto a matsayin zababben shugaban kasa wanda zai dauki madafun ikon kasar a watan Oktoba da ke tafe.

https://p.dw.com/p/4f7kK
Prabowo Subianto zababben shugaban kasar Indonesiya
Prabowo Subianto zababben shugaban kasar IndonesiyaHoto: Oscar Siagian/Getty Images

A wannan Laraba, hukumar zaben kasar Indonesiya ta tabbatar da Prabowo Subianto a hukumance a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar, inda zai dauki madafun iko a matsayin shugaba na gaba a kasar ta uku wajen girman tsarin dimukaradiyya a duniya.

Subianto mai shekaru 72 da haihuwa zai karbi ragamar kasar a watan Oktoba, daga hannun Shugaba mai barin gado Joko Widodo wanda yake da farin jini. Shi dai Prabowo Subianto ya samu nasara a zagayen farko inda ya doke sauran 'yan takara biyu, tare da samun fiye da kashi 50 cikin 100 na kuri'un da aka kada, kuma adadin da ake bukata wajen kauce tafiya zagaye na biyu.