1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Rasha ta soki yadda aka yarda da yunkurin tsige Trump

Abdoulaye Mamane Amadou
December 19, 2019

Shugaban kasar Rasha ya soki hujjojin da majalisar dokokin Amirka ta yi amfani da su har ta kai ga jefa kuri'ar na'am da matakin shirye-shiryen tsige shugabana Donald Trump.

https://p.dw.com/p/3V5hw
Russland Putin Jahres-PK 2019
Hoto: picture-alliance/dpa/Sputnik/A. Druzhinin

Shugaba Vladimir Poutine na magana ne a yayin wani taron bita kan dangantakar Amirka da Rasha, inda ya kara da cewa cece-kucen da ake fuskanta a Amirka wata siyasa ce kawai ta cikin gida, kana kuma ya ce ba tun yau ba jam'iyyar democrate ke neman sale salin samun sakamakon zabe ta ko halin kaka, kana wasu daga cikin dalilan da ya sa ta bullo da zargin katsalandan din Rasha a zaben Amirka a baya, kan daga bisani ta bullowa shugaba Trump da wannan sabuwar bazata. 

A yanzu dai kallo ya koma kan majalisar dattijai ta Amirka inda shugaban kasar yake da gagarumin rinjaye, domin ganin ko 'yan majalisun za su aminta da jefa kuri'ar, wanda hakan kawai ne ka iya tabbatar da tsige shugaban ko akasin haka.