1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sakataren harkokin wajen ya soke ziyara a Jamus

Abdoulaye Mamane Amadou MNA
May 7, 2019

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo ya bayyana matakin soke wata ziyarar aiki a Tarayyar Jamus, ziyarar wacce a ka'idance za ya gana da shugabar gwamnati Angela Merkel da sauran mukarraban gwamnati.

https://p.dw.com/p/3I5DO
US-Außenminister Mike Pompeo
Hoto: Getty Images/L. Balogh

Ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta bayyana matakin soke ziyarar babbar sakataren harkokin wajenta Mike Pompeo da a ka'idance a yau Talata ne sakataren Mike Pompeo zai gana da Merkel, kan daga bisani ya tattauna da takwaransa na harkokin wajen Jamus Heiko Maas.

Sai dai da take magana kan dage ziyarar, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amirka ta ce an dage ziyarar ta Pompeo ba tare da ta bayar da wasu hujjoji ba, sai dai kakakin ma'aikatar ta ce zai kai ziyara a birnin London gobe Laraba , sannan kuma zai ziyarci takwaransa na kasar Rasha Sergueï Lavrov  a ranar 14 ga wannan watan a wata ziyarar da zai kai a kasar.