1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Iran ce ta kai hari a Saudiyya inji Pence

Abdullahi Tanko Bala
September 17, 2019

Sakataren harkokin wajen Amirka Mike Pompeo zai je Saudiyya domin tattauna martanin Amirka kan harin da aka kai wa rijiyoyin man saudiyya wanda aka dora alhakinsa akan Iran.

https://p.dw.com/p/3PkI9
Saudi-Arabien Abqaiq Feuer in Aramco Raffinerie
Hoto: Reuters

Mataimakin shugaban Amirkar Mike Pence yace sakataren harkokin wajen Mike Pompeo zai je Saudiyya domin tattauna martanin da Amirka ke shirin dauka. Yana mai cewa Amirka bata bukatar yaki da kowa amma a shirye ta ke a kowane hali domin kare muradunta da na kasashe aminanta.

Tun da farko wani jami'in Amirka da ya bukaci a sakaya sunansa yace Amirka ta tabbatar da cewa makamai masu linzami da suka fada cibiyoyin man na Saudiyya an harba su ne daga cikin kasar Iran.

Shugaban Iran Hassan Rouhani yace harin wanda yan tawayen Houthi suka kai wani mataki ne na kare kai.

A halin da ake ciki kuma farashin danyen mai ya fadi a wannan talatar bayan da manazarta suka ce ana tsammanin Saudiyya za ta farfado da yawan man da ta ke hakowa bayan harin jirage marasa matuka da aka kai mata.