Paris na goyon bayan matakan Soji a Mali
August 4, 2012Ministan tsaro na Faransa Jean-Yves Le Drian, ya shaidar da cewar ƙasarsa za ta bada goyon bayanta wa yunƙurin ƙasashen Afirka na amfani da ƙarfin soji a yankin arewacin Mali da ke hannun 'yan tawaye. Sai dai duk da cewar yana da imanin hakan ya kasance wajibi, kuma akwai bukatar yinsa, Faransa ba zata kasance a sahun gaba ba. A ziyarar da ya kai birnin Lorient dake yanki arewa maso yammacin Faransa, ministan tsaron kasar ya faɗa wa manema labaru cewar, ƙasarsa bata da hurumin ƙirƙirar amfani da sojoji a Mali. Le Drian ya kara da cewar, Faransa na muradin kasashen ECOWAS da Tarayyar Afirka ta AU, su tsara shirin. Yace amfani da karfin soji a arewacin Mali ya zama wajibi, domin kasarsa a shirye take ta bada goyon bayanta, ya kuma yi fatan tarayyar turai zata bada nata goyon bayan, bisa la'akari da halin da yankin ke ciki.
Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Usman Shehu Usman