1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Takaddama tsakanin Pakistan a Indiya a kan Kashmir

Musch Borowska, Bernd USU
August 15, 2019

Rahotannin sun tabbatar da cewar an soma gwabza yaki tsakanin Pakistan da Indiya a kan rikicin mallakar yankin Kashmir. Wannan shi ne karo na uku da kasashen biyu ke gwabza yaki a kan yankin.

https://p.dw.com/p/3NynN
Nato Truppen Afghanistan Pakistan Anschlag Taliban
Hoto: Reuters

A yayin da kasashen Indiya da Pakistan ke yin bukukuwan shekaru 72 na samun 'yancin kai, a yankin Kashmir kuwa, sabuwar kuntata wa jama'a ce aka bullo da ita. Tun yakin da aka gwabza tsakanin kasashen Indiya da Pakistan a shekara ta 1947 izuwa 1949, aka raba yankin na Kashmir gida biyu, inda daya bangaren ke karkashin Indiya yayin daya bangaren ke karkashin Pakistan. Tuni ma da yaki ya barke tsakanin kasashen biyu, inda kafin hada wannan rahoton, labarai suka tabbatar da mutuwar sojojin Pakistan uku yayin da sojojin Indiya biyar suka mutu a gumurzun da kasashen biyu suka yi.