1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

OPCW ta kammala bincikenta a Siriya

Ramatu Garba Baba
May 4, 2018

Tawagar kungiyar da ke yaki da bazuwar makamai masu guba ta duniya OPCW, ta ce ta kammala binciken da ya kai ta Siriya don tantance zargin yin anfani da sinadarin gas a harin da aka kai a garin Douma da ke yankin Ghouta.

https://p.dw.com/p/2xCKz
Niederlande Eingang der OPCW
Hoto: Getty Images/AFP/J. Thys

Tawagar ta koma ofishinta da ke kasar Holland inda daga nan ne za ta shirya rahoto kan sakamakon binciken. Kungiyar ba ta da ikon fadin sakamakon binciken na ta.

Ma'aikatar harkokin wajen Rasha ta bakin mai magana da yawunta Maria Zakharova ce ta sanar da hakan. A ranar bakwai ga watan Afrilun aka kai hari da makami mai guban a garin na Douma da a wancan lokacin ke karakashin ikon 'yan tawaye, kasashen yamma sun zargi dakarun Rasha da na gwamnatin Siriya da laifin anfani da makamin da dokar kasa da kasa ta haramta akan farraren hula.

An kuma zargi kasashen biyu da yunkurin hana tawagar masana masu aikin binciken shiga yankin na Douma bayan faruwar lamarin, an shirya daukar matakin aza takunkumi kan wadanda aka samu da laifin hannu a al'amarin da ya salwantar da rayukan mutane kusan dari ciki har da yara kanana.