1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Olaf Scholz na Jamus zai gana da shugaban Argentina Milei

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 23, 2024

Argentina dai na da dinbin arzikin sinadarin Lithium, wanda Jamus ke matukar bukata domin bunkasa harkokin makamashinta

https://p.dw.com/p/4hOcq
Hoto: Abdulhamid Hosbas/AA/picture alliance

Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz zai karbi bakuncin shugaban Argentina Javier Milei a Lahadin nan a birnin Berlin, inda ake sa ran za su tattauna batutuwan da suka shafi ci gaban tattalin arziki a tsakanin kasashen biyu.

Karin bayani:COP28: Scholz ya gabatar da kokarin Jamus kan muhalli

Ganawar shugabannin biyu masu ra'ayoyi da ke cin karo da juna, za ta mayar da hankali kan batun kasuwanci marar shinge, tsakanin kungiyar tarayyar Turai EU da kungiyar bunkasa tattalin arzikin kasashen kudancin Amurka.

Karin bayani:Taron tattalin arziki tsakanin Turai da Afirka

Tun da fari dai an tsara yi wa Mr Milei tarba da faretin sojoji tare da taron manema labarai, amma aka soke hakan a cikin kankanin lokaci.

Argentina dai na da dinbin arzikin sinadarin Lithium, wanda Jamus ke matukar bukata domin bunkasa harkokin makamashinta.