1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Obama ya goyi bayan takarar Kamala Harris

Abdullahi Tanko Bala
August 21, 2024

Tsohon shugaban Amurka Barrack Obama ya bai wa yar takarar shugabancin kasa ta Jam'iyyar Democrats Kamala Harris gagarumin goyon baya a yayin da ya gabatar da Jawabi a babban taron jam'iyyar

https://p.dw.com/p/4jiRZ
Barack Obama a babban taron Jam'iyyar  Democrats
Hoto: Eva Hambach/AFP/Getty Images

Obama ya shaida wa dandazon jama'ar da suka halarci taron cewa Amurka ta shirya wa sabon babi da jin labari mai armashi da kuma shirya karbar shugaba Kamala Harris.

Obama ya kuma soki Donald Trump na Jam'iyyar Republican wanda ya gaje shi wanda kuma zai fafata da Kamala Harris a takarar neman kujerar shugabancin Amurka.

Tun da farko a ranar Talata 'yan Jam'iyyar Democrats sun tabbatar da Kamala a matsayin 'yar takarar shugabar kasa a karkashin inuwar Jam'iyyar a zaben da za a yi ranar 5 ga watan Nuwamba.

A ranar Alhamis Kamala Harris za ta gabatar da jawabi ranar da za a kammala taron na kwanki hudu.