1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Norway za ta shiga siyasar Venezuela

May 18, 2019

Shugaba Nicolas Maduro na kasar Venezuela, ya yi marhabin da shirin da kasar Norway ta bijiro da shi na tattaunawa tsakaninsa da madugun adawar kasar Juan Guaido.

https://p.dw.com/p/3Ih8S
Venezuela Krise | Nicolas Maduro, Präsident in Caracas
Hoto: Reuters/Miraflores Palace

Shugaba Maduro ya ce an kama hanyar samun kwanciyar hankali da ci gaba, saboda hakan ne yake bukatar goyon bayan al'umar Venezuela, lokacin wani biki da aka yi a gaban dakarun kasar 6,500. Kasar Norway ta sanar da tuntubar bangarorin na Venezuela masu jayayya da juna.

Sai dai a ranar Alhamis da ta gabata madugun adawa Mr. Guido, ya musanta cewar akwai wani shiri na tattaunawa, ko da yake ya amince cewar akwai jami'an kasar Norway da ke kokarin kawo sulhu a tsakanin nasu.

Venezuela mai arzikin mai, ta shiga rudanin siyasa da wasu manyan kasashe ke da ra'ayi a ciki.