1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Noman auduga a Burkina Faso

December 14, 2005

Kasar Burkina Faso ta dogara ne kacokam akan noman auduga wajen samun kudaden shiga

https://p.dw.com/p/BvSG
Masu zanga-zanga a Hong Kong
Masu zanga-zanga a Hong KongHoto: AP

Tattalin arzikin Burkina Faso ya dogara ne kacokam akan auduga, wacce ta kama kashi biyu bisa uku na jumullar kayayyakin da kasar ke cinikinsu a ketare. To sai dai kuma ko da yake bana an kiyasce yawan audugar da zata noma zai kai tan dubu 700, amma hakan ba zata taimaka wajen kyautata matsayin rayuwar manoman kasar ba. Dalili kuwa shi ne ci gaba da tabarbarewar farashin audugar da ake fama da ita a kasuwannin duniya sakamakon makudan kudi da Amurka ke kashewa domin karya farashin audugar da manomanta ke samarwa. An ji daga bakin Kahoun Jean Bosco, daya daga cikin manoman auduga a Burkina Faso yana mai bayanin cewar a bara sun sayar da audugar da suka noma akan CFA 210 kowane kilo daya, amma a wannan shekarar farashin ba zai zarce CFA 175 akan kowane kilo ba, lamarin dake ma’anar hasara ga manoman. Kahoun Jwan Bosco dake da shekaru 54 da haifuwa sai da ya hada da sayar da masarar da ya tara a rumbu domin samun kudin biyan mataimakansa kuma abin da yake sa ran zai samu daga audugar idan kaka tayi albarka ba zai wuce kwatankwacin dala 536 daga gonarsa ta auduga mai fadin eka daya da rabi ba. Kasar Amurka, wacce tafi kowace kasa noman auduga a duniya ta kashe abin da ya kai dala miliyan dubu hudu da rara domin karya farashin audugar da manomanta suka samar a shekara ta 2004. Wannan kudi kuwa ya ribanya kasafin kudin kasar Burkina faso baki daya. Wani bayanin da gamayyar kasashen Afurka dake samar da auduga ta bayar ya nuna cewar kasashen na Afurka sun yi asarar abin da ya kai dala miliyan 400 tsakanin shekara ta 2001 da ta 2003 sakamakon ire-iren wadannan matakai na karya farashin audugar da kasashe masu ci gaban masana’antu na Turai da Amurka kev dauka. A taron kungiyar ciniki ta kasa da kasa WTO da ake gudanarwa yanzu haka a Hong Kong kasashen Afurka 33 dake noman auduga zasu gabatar da wata takardar kara dake da hannun mutane sama da miliyan biyu domin kiran kawo karshen wannan mataki na karya farashin audugar a cikin gaggawa. Tuntuni dai kungiyar WTO tayi Allah waddai da matakin tallafin da Amurka ke dauka. Kasashen Afurka masu noman auduga kamar Burkina Faso da Mali da Benin da Chad na fatan ganin an kawo karshen wannan mataki na karya farashin amfanin da manoman kasashe masu ci gaban masana’antu ke fitarwa zuwa ketare, nan da karshen shekara. Duk da bunkasa noman auduga da suka yi a cikin shekaru goma da suka wuce, amma har yau kasashen Afurka ba su fara cin gajiyar ta ba. Ita kanta Burkina Faso tayi asarar abin da ya kai dala miliyan 35 daga cinikin audugar da tayi a shekarar da ta wuce. Ta la’akari da haka kasashen Afurka masu noman auduga zasu sa ido akan taron kungiyar WTO a Hong Kong domin ganin ko Ya-Allah sakamakonsa zai haifar musu da wani da mai ido akan manufa.