1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Nikki Haley na shirin janyewa daga neman shugabancin Amurka

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 6, 2024

Wannan mataki zai bai wa tsohon shugaban kasar Donald Trump damar zama 'dan takara tilo na jam'iyyar Republican, lamarin da zai ba shi damar kalubalantar shugaba mai ci yanzu Joe Biden a karo na biyu a jere

https://p.dw.com/p/4dEBN
Hoto: Carolyn Kaster/AP Photo/picture alliance

Kafofin yada labaran Amurka da suka hada da Wall Street Journal da CNN, sun bayyana cewa mai neman takarar shugabancin kasar Nikki Haley na shirin sanar da janyewa daga neman takara a jam'iyyar Republican.

Karin bayani:DeSantis zai kalubalanci Trump a Amirka

Dama dai tsohuwar jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya ta sha kaye a hannun Donald Trump a akasarin jihohi da aka yi zaben fidda gwani a "Super Tuesday".

Karin bayani:Jakadar Amirka a Majalisar Dinkin Duniya ta yi murabus

Kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito cewa za ta gabatar da jawabin nan ba da jimawa ba daga garinta na Charleston, da ke jihar South Carolina.

Wannan mataki zai bai wa tsohon shugaban kasar Donald Trump damar zama 'dan takara tilo na jam'iyyar Republican, lamarin da zai ba shi damar kalubalantar shugaba mai ci yanzu Joe Biden a karo na biyu a jere.