1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Babu jakkai a bisa kasuwani

September 24, 2019

 Shekaru hudu ke'nan da hukumomin Nijar suka haramta kasuwancin jakkai daga Nijar zuwa wasu kasashe saboda barazanar karewa da suke fuskanta a cewar hukumomin.

https://p.dw.com/p/3Q9Nr
Mann auf einem Esel in Zinder, Niger
Hoto: DW/M. Kanta

 Daga daukar wannan doka a shekara ta 2016 zuwa yanzu kasuwancin jakkai a Nijar musamman a Maradi ya shiga cikin wani mawuyacin hali abin da ya jefa 'yan kasuwar jakkan da masu kiwon da sauran masu ci cikin harkar kasuwancin  jakkan cikin matsaloli dabam-dabam. A bisa daukacin kasuwanin Maradi ba a samun jakkan kamar yadda aka saba gani a da, kana kuma farashinsu da a da ya tashi yanzu ya fadi saboda rishin ciniki.