1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama wani dan Libiya mai sarafar baki

December 30, 2022

An cafke wani dan kasar Libiya mai shekaru 29 da ake zargi da jagorantar safarar bakin haure da ke bi ta Nijar zuwa Turai.

https://p.dw.com/p/4LaWv
USA am Grenzübergang El Paso
Hoto: John Moore/Getty Images/AFP

An kama mutumin ne bayan wani bincike na hadin gwiwa tsakanin 'yan sandan Nijar da Faransa da Spain kamar yadda wata majiyar 'yan sandan Faransa ta bayyana. Wanda ake zargin,wanda aka kama a ranar 20 ga watan Disamba a Agadez, a arewacin Nijar,ya ba da tabbaci a lokacin sauraren karar da masu binciken suka yi masa cewa, ya rika aika ‘yan ci-rani sittin a mako har tsawon shekaru bakwai. Galibinsu daga kasashen yankin yammacin Afirka da tsakiya, wadanda da farko ake kai su Nijar cikin motocin daukar kaya, tare da kaucewa manyan birane. Daga nan a wuce da su zuwa Libiya ko  Aljeriya, kafin a tsalaka da su zuwaTurai. Arewacin hamadar Nijar ya yi kaurin suna wajen safarar bakin haure da muggan kwayoyi da makamai sannan kuma yana tattare da kungiyoyin masu jihadi.