1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Turai za ta taimaka wa jamhuriyar Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou RGB
May 20, 2021

Manyan kasashen duniya tare da Babban Bankin Duniya, sun sha alwashin tallafa wa jamhuriyar Nijar don ganin ta farfado daga masassarar da ta fuskanta daga annobar corona.

https://p.dw.com/p/3tfvC
Nigeria Präsidenten  Mohamed Bazoum
Shugaba Mohamed BazoumHoto: Facebook/Präsidentschaft der Republik Niger

Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum na daya daga cikin shuwagabannin nahiyar Afirka fiye da 20 da suka halarci taron kolin da Faransa ta shirya kan farfado da tattalin arzikin nahiyar da annobar corona ta yi wa illa a birnin Paris. Manyan kasashen duniya dai ciki har da Asusun bayar da Lamuni na Duniya IMF  da Bankin Duniya, sun aminta da dafawa kasashen nahiyar da mukadan kudade na ganin sun farfado daga dogon suman da suka yi a sakamakon ta'asar annobar corona. Karin Bayani    Bazoum zai yi aiki da kasashe makwabta

Daman ya ci karo da masassarar tattalin arzikin da nahiyar ke fama, Nijar na daya daga cikin kasashen da za su ci gagarumar riba ga wannan mataki kamar yadda Shugaban kasar Mohamed Bazoum ya sheda. Shugaban dai bai yi karin bayani a game da karbar rance daga Asusun Lamuni ba, a tattaunawar da ya yi da tashar DW.

Karin Bayani  IMF: Rance domin yakar COVID-19 ga kasashe
Bayan kammala taron kolin dai shugaban na Nijar ya kuma ziyarci wasu kasashen nahiyar Turai ciki har da Luxembourg da Beljiyam, kana kuma ya tattauna da Kungiyar Tarayyar Turai wacce ta yi alwashin dafawa Nijar kan fannoni da dama duba da yadda suka gamsu da sauyin mulkin dimukuradiyar da aka yi a wannan kasa da ke yankin yammacin Afirka a cikin ruwan sanyi ba tare da an sami tashin hankali kamar yadda aka saba gani a wasu kasashen da ke nahiyar ba, lamarin da ke zaman irinsa na farko a tarihi. Tun bayan 

Karin Bayani    Kokarin warware matsalar ilimi a Nijar
Al'ummar Jamhuriyar ta Nijar da dama sun bayyana gamsuwarsu, dangane da yadda sannu a hankali Shugaba Bazoum na daukar matakai da ke zama tamkar na cinnaka wanda bai san na gida ba a fannin yakar cin-hanci da rashawar da ake ganin, na daya daga cikin matsalolin da suka hana ci gaban kasar. Ko da yake wasu na ganin cewa ba a saurin yabon danyen mai sai an jira rana ta yi an ga yadda ya kasance, domin kuwa gwamnatocin da suka shude a Nijar na kudirar aniyar wannan kokowa ta cin hanci amma daga karshe labarin ya zamo na shafa labarin shuni.