Nijar: Yarjejeniyar shirya zabe cikin lumana
January 28, 2016A Jamhuriyar Nijer 'yan adawar kasar ne suka yi fatali da tayin rattaba hannu a kan wata yarjejenya ta bai daya da ta shafi jam’iyyun siyasa domin ganin an yi zabe lafiya an kare lafiya wato (code de bonne conduite a Faransance). 'Yan adawar sun kauracewa saka hannu a kan yarjejeniyar ne suna masu cewar ba za ta tsinana komai ba ganin irin take taken da gwamnatin kasar ke yi cikin shirin zaben.
Kundin mai dauke da ayoyi akalla 55 kumshe yake da shikashikkai uku dake da matukar mahimmanci gaske a zabubukan da kasar za ta tunkara wadanda suka shafi rawar da 'yan siyasa kan iya takawa ta hanyar amfani da dubarorin kauce wa fitina da kalamai maras kyau a yayin yakin neman zabe, har ma ga zuwa yada akidun na zaman lafiya da salama da aika wakilai a runfunan zabe da kuma bai wa jami’an tsaro hadin kai domin zartar da aikinsu a ranar zabe, da ma runguma da kaddara kan abinda zai iya biyowa bayan zabe muddin aka wallafa ko hukumar zabe ta bayar da sakamakon
'Hujjar adawar Nijar ta yin watsi da tayin shirya zabe cikin lumana
Sai dai a yayin da aka zo rattaba hannu a kan wannan sabon kundin na wannan shekarar kawancen jam’iyyun adawa fitowa fili ya yi ya ce a kai kasuwa. Hon Tidjani Abdoulkadri Sakataren jam’iyyar Mnsd ne mai adawa
" Ba sa cikin yanayin tsara zabe kamar yadda kundin tsara zabe ya tanada. To kenan ba za ta yiwu ba ku zo ku sa hannu ga takardar da tun kafin a tashi an saba wa wadannan dokokin don shi ne muka yi allah wadawarai da wannan yarjejeniyar muka ce to tunda su sun riga sun taka dokoki mine ne tasiri da mahimmancin yarjejeniyar da tuni aka taka dokokin zabe".
Rashin saka hannu a kan sabon kundin dai da 'yan adawar suka yi a yammacin jiya ya haifar da jera manya-manyan ayoyin tambaya ga irin yadda makomar zaben da za’a yi za ta kasance ganin irin yadda fagen siyasar na Nijer ya turnike da hayaniya da kura irin ta 'yan siyasa.
'Yan majority sun dora ayar tambaya kan manufar 'yan adawa a zabe
Sai dai a cewar kakakin kawancen jam’iyyun da ke mulki daya bangaren da ya rattaba hannu a kan kundin zaben na tafe ba zai haifar da fargaba ba ganin yadda akasarin jam’iyyun suka yi wa kundin lale marhabun,
Alhaji Yve Ali Tosa shi ne kakakin kawancen masu mulki na MRN
"Ya ce abin da ban mamaki kenan da awkai wata makarkashiya da suka ajiye a kanunsu amma karen da ya sha kwai a kansa take karewa ba za’ayi zabe a cikin hatsaniya ba domin ko da ba su saka hannu mun yarda da abin da wannan dokar ta tanada"
'Yan adawa dai na zargin jam'iyyar PNDS Tarayya da taka ayar doka mai lamba 21 ta kundin tsarin zabe "code electoral" ta hanyar shiga yakin neman zabe gadan-gadan musamman ma shugaban kasa inda 'yan adawar suka ce yana furta kalamai irin na gangamin siyasa alhali kuwa kundin tsarin zabe ya hana aikata hakan Inji Tidjani Abdoul kadri na jam’iyyar Mnsd Nassara
"Ya ce da rigarshi ta shugaban kasa ya maida rigar kauye ya shiga yekuwar zabe yau kusan sati biyu yana yawo a cikin kasa ba inda bai je ba a cikin wannan kasar kuma mu muna ganin wadannan halaye ne na taka da maida dokoki gefe".
Sai dai har gobe jam’iyyar Pnds Tarayya da kawancenta na ci gaba da musanta kalaman na kawancen jam’iyyun adawa suna masu cewa shugaban na ziyara ne kawai don duba ayyukan da ya yi wa al’umma.
"Ya ce dole ne shugaban kasa ya je ya ga al’ummarshi kuma ba’a kayyade mashi lokacin zuwa ganin al’ummar shi ba a’a, to ko mi ya sa sai yanzu a yayin da ake jajibirin zabe a cewar su? Ai ko wane abu ka’ida gare shi domin yanzu ne ayyukan suka kare"
Ko da yake har yanzu Nijer ba ta taba fuskantar hargitsi ko fitina mai nasaba da zabe ba, a shekarar 2011 ma akalla jam’iyyun siyasa 36 ne suka rattaba hannunsu a kan wani kundin makamancinsa inda hakan ta bayar da dama aka yi zabe a cikin tsanaki da kwanciyar hankali.
Nijer dai na sahun kasashen farko a yammacin Afirka na wannan shekarar da za’a gudanar da zabe, zaben da da yawa 'yan kasar ke ganin za ya iya kasancewa na farko a tarihi ganin irin yadda takon sakar 'yan siyasa ke kara zafafa