1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron makiyayan Afirka a Nijar

Gazali Abdou Tasawa LMJ
May 28, 2021

A Jamhuriyar Nijar an fara wani taron kasa da kasa na kungiyoyin makiyayan Afirka kan yadda matsalolin tsaro ke yin illa ga sana'ar kiwo da rayuwar makiyaya.

https://p.dw.com/p/3u82q
Niger Normaden Fulani Scharfherde bei Gadabeji
Fulani kan yi yawo waje-waje domin samar wa dabbobinsu abinciHoto: AP

Taron wanda kawancen kungiyar makiyaya na Billital Maroobeya ya shirya, tare da hadin gwiwar gwamnatin Jamhuriyar ta Nijar da kungiyoyin kasa da kasa da suka hadar da kungiyar Tarayyar Turai da kuma Babban Bankin Duniya, ya samu halartar kungiyoyin makiyaya da sarakunan gargajiya daga kasashe bakwai na yankin Sahel da Afirka ta Yamma.

Karin Bayani: Fulani ba ma su garkuwa da mutane ne ba

Makasudin taron shi ne bitar halin da matsalolin tsaro suka jefa rayuwar makiyaya da yin barazana ga makomar sana'ar kiwon a wadannan kasashe na Afirka. Malam Abdou Neino Gajango shi ne shugaban kungiyar mutanen karkara ta FENAP, guda daga cikin mahalarta taron ya bayyana cewa makiyaya sun shiga tsaka mai wuya a yakin da ake tsakanin sojoji da 'yan ta'adda.

Nigreria Fulani-Nomaden
Makiyaya na fama da matsaloli a AfirkaHoto: AFP/Luis Tato

Taron ya samu halartar sarakunan gargajiya na yankunan makiyaya. Malam Hadi Gurgudu Sarkin Fulanin jihar Damagaram, ya bayyana cewa hatta su kansu sarakunan gargajiya ba su tsira daga wannan matsala ta ta'addanci ba. Sai dai Malam Labdo Ousmane guda cikin shugabannin kungiyoyin makiyaya daga Tarayyar Najeriya, ya ce akwai bukatar makiyayan su fahimta tare da kiyaye dokokin kasashen baki daya, wanda hakan zai ba su damar gudanar da kiwon nasu  ba tare da matsala ba.

Karin Bayani: Rikicin Fulani da Makomar kiwo a Najeriya

Wadannan matsalolin tsaro dai, na ma yin barazana ga makomar sana'ar kiwon a kasashen Afirka baki daya. A Asabar din karshen mako ne dai ake kammala wannan zaman taro, wanda a karshensa ake sa ran mahalartan za su fito da shawarwari na hanyoyin shawo kann wannan matsala ta tsaro ga sana'ar kiwo, shawarwarin da za a gabatar da su ga shugabannin kasashen Afirka.