1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Taron koli kan matsalar cirani

Abdoulaye Mamane Amadou
March 16, 2018

Hukumomin kasashen Turai masu karbar baki 'yan gudun hijira tare da wasu kasashen Afirka sun samar da mafita a Yamai kan matsalolin gudun hijira.

https://p.dw.com/p/2uSpZ
Frankreich PK Migrationsgipfel in Paris
Hoto: Getty Images/AFP/L. Marin

Ministocin harkokin kasashen Italiya da Fransa da Spaniya da Jamus ne suka halarci taron irinsa na farko don samar da mafita da tokororinsu na kasashen Cote d’ivoire da Mali da Senegal da Guniea da Nijar hada da Burkina Faso da zimmar duba hanyoyin kara inganta yaki da matsalolin bakin haure da safarar mutane da ke addabar bangarorin biyu.

Niger Ibrahim Yacouba
Ministan harkokin wajen Nijar, ibrahim YacoubaHoto: DW/Abdoulaye Mamane Amadou

Ministan harkokin wajen Jamhuriyar Nijar Malam Ibrahim Yacouba ya ce "abinda gwamnatocin kasashen mu ke magana shi ne na wadanda ke fitowa su wuce ba kan ka’ida ba saboda hakan duk wadanda muka tara daga nan din nan daga inda mutanen ke fitowa ne har inda suke wucewa."

Niger Agadez Sahara Flüchtlinge Wasser
Wasu 'yan gudun hijira cikin hamadar saharaHoto: Reuters/Akintunde Akinleye

Kasashen yankin Sahel kamar su Moritaniya da Chadi da Libiya inda a yanzu fiye da 'yan Afirka bakin haure fiye da dubu 15 ke makale sun halarci taron kolin kasahen sun cimma matsaya hada gwiwa domin kauda mutanen da ke safarar bil Adama da kuma samar wasu dabarun ciki har da shimfida babban tsari na bai daya tsakanin kasashen.
 
Kasashen Faransa da Jamus da sauran kasashen Turai da suka halarci taron kolin sun sha alwashin baiwa kasashen yammacin Afirka tallafi mai tsoka domin dakile matsalar tun daga tushe tare da taimakawa kasar Nijar wacce ke a matsayin babbar kofa ta shiga zuwa Turai ta barauniyar hanya.

Migranten in Agadez
Wasu matasa bakin haure a AgadezHoto: DW/K. Gänsler

Jekadan Kasar Jamus a Nijar Münchow-Pohl ya ce "Jamus ta dauki alkawuran tallafawa Nijar ta fannoni da dama musamman fannin sufuri da tsaro domin ganin kasar ta kara matsa lamba don ceto dubban jama’a da ke halaka a cikin Sahara da teku." Alkalumma dai sun ce an samu ragowar kwarar bakin haure fiye da kima da ke ficewa ta Nijar zuwa Turai, inda a yanzu ba a wuce mutune dubu 5,500 ba kawai ake samu a wata sabanin dubu 5,000 zuwa 7,000 da ke tsallakawa a duk mako.