1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Nijar ta saye hannun jarin bankin musulunci a Niamey

Gazali Abdou Tasawa
October 8, 2024

Gwamnatin Nijar ta saye hannun jarin bankin muslunci na kasar a wani yunkuri na samar da ‘yancin kanta a fannin hada-hadar kudi da bunkasa tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/4lYQt
Babban bankin musulunci IDB a birnin Jiddah
Babban bankin musulunci IDB a birnin JiddahHoto: picture-alliance/Arcaid/R. Bryant

A baya dai Babban Bankin Raya kasashen Musulmi na Duniya ne wato BID ke rike da kaso 57 cikin dari a yayin da reshen sa na  Bankin tamweel Africa Holding ke mallakar kaso 35 cikin dari na hannun jarin Babban Bankin Muslunci na kasar Nija  wanda aka kafa a shekara ta 1983r. To sai dai a yanzu gwamnatin mulkin sojan kasar ta Nija ya saye kaso 95 cikin dari na hannun jarin Bankin Muslunci wanda ya koma a karkashin ikon kasar ta Nijar. Kuma Malam Soly Abdoulahi masalin ilimin tattalin arziki a Nijar ya ce matakin zai taimaka wa Nijar samun ‘yanci a fannin hada-hadar kudi tsakanin bankuna da kuma rage dogaro da wasu bankunan kasa da kasa.

Shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahamane Tiani cikin fararen kaya
Shugaban mulkin sojin Nijar Abdourahamane Tiani cikin fararen kayaHoto: Gazali/DW

"Bayan an kada gwamnatin Bazoum ai ka ga irin yadda CEDEAO da UEMOA suka dauki matakin da ya sa Babban Bankin BCEAO ta dakatar da zubo kudi cikin Nijar. Sai aka yi ta samun matsala tun da gwamnati ba ta samun kudaden gudanar da ayyuka haka ‘yan kasuwa ba sa samun kudaden gudanar da harkokinsu,domin duk wadannan bankuna suna bin umurnin kasashen waje ne da kuma wadannan kungiyoyi. To in ya zamo a yanzu Nijar na da banki na kanta, duk wata manakisa da za a nemi a yi mana kan harkar kudi ba za ta yi tasiri ba saboda gwamnati na da kudinta aje a cikin banki"

Tuni dai babban dakin shawara na ‚yan kasuwan Nijar na Chambre des Commerce ta bakin shugabansa Malam Moussa Sidi ya bayyana gamsuwarsa da matakin gwamnatin na saye wannan Bankin na Muslunci wanda ya bayyana fatan zai taimaka wa ‘yan kasuwa musamman a fannin sassauci kudin ruwa wajen bayar da bashi.

Shugaban Nijar Abdourahamane Thiani
Shugaban Nijar Abdourahamane ThianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP/Getty Images

"Bankin ya taimaka wa ‘yan kasuwa da ma gwamnati inda za ya dunga bashi ba da kudin ruwa mai yawa ba. Domin bankunan da ake da a yanzu wasu na dora kudin ruwa na kaso 15 har ma 16 cikin dari. Shi kuma duk wanda ya dauki bashi da irin wannan kudin ruwa to da wuya ya samu wata riba. Dan haka nake ganin wannan babban albishir ne domin idan dai ya zamo banki ne na kasa dole zai kula da hakkin kasa"

Gwamnatin Nijar ta saye hannun jarin Babban Bankin Islamar na BIN ne a daidai loakcin da sannu a hankali tsarin Bankunan Muslunci ke kara tasiria cikin harkokin kudi da na kasuwanci a kasashen duniya da dama. Sai dai Malam Hassan Gamkale masanin dokokin Islama ya ce akwai bukatar ‘yan kasa su fahimci tsarin aikin Bankunan Islama kafin neman yin hulda da su.DOC

Firaministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine
Firaministan Nijar Ali Mahamane Lamine Zeine Hoto: Balima Boureima/Anadolu Agency/picture alliance

"Bankin Islam shi na iya tafiya da ‘yan Nijar da dokokin Nijar cikin sauki ga Musulmi da ma wanda ba Musulmi ba. Amma iina son mutane su gane cewa ba dan an ce bankin Muslunci ba, babu bankin duniya da bas hi yin sana'a domin ya ci riba. Babbanci bankin Islama da na jari hujja da sauran bankoki sauki ne, amma kos hi shina sa riba. Dan haka ya kamata Nijar ta sa kwararrin ma'aikata wadanda suka san abin da ake cewa addini a cikin doka"

Abin jira a gani dai a nan gaba shi ne tasirin da sayen Babban Bankin Islama zai yi a nan gaba wajen bunkasa tattalin arzikin Nijar da samar mata da cikakken ‘yancin a fannin hada-hadar kudi.