1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta ce yankin iyakar ta da Burkina Faso na ta ne

October 17, 2012

Jamhuriyar Nijar ta gabatar wa kotun duniya da ke birnin Hague na Holland hujjojin da ke nuna cewa yankin da ke kan iyakarta da Burkina Faso mallakinta ne. Rikicin kan iyakan tsakaninsu ya kwan biyu.

https://p.dw.com/p/16Rgb
Gebäude des Parlaments der Republik Niger, Niamey. Foto: Mahaman Kanta/DW, 19.5.2011, Niamey / Niger, Zulieferer: Thomas Mösch
Gebäude der Nationalversammlung in Niamey NigerHoto: DW

Jamhuriyar Nijar da Burkina Faso na jayeyya ne akan iyakar da ke tsakaninsu, wadda turawan mulkin mallaka na kasar Faransa suka shata tun 1927. Kasashen biyu sun kasa samun daidaito iyakar ta su bayan da suka samu 'yancin kaai daga Turawan da suka yi musu mulkin mallaka. Duk wani yunkurin da suka yi ta yi domin magance matsalar tsakaninsu ya ci tura. Saboda suka shigar da kara gaban kotun duniya domin ta warware wannan rigimar dake tsakanin su.


Nijar ta dogara akan tarihi domin kare matsayinta a kotun birnin Hague

Ministan harkokin wajen Nijar Mohamed Bazu, shi ya jagorancin tawagar kasarsa a akotuin da ke birnin Hague na Holland. Ya ce "akwai garuruwa da yawa wanda kasar Burkina Faso ta ce na ta ne. Amma suka ce ba daidai ba ne a raba gari ko gunduma biyu. Alhali tun lokacin turawan da suka yi wa kasashen biyu mulkin mallaka ba su taba raba gari ko gunduma biyu."

Shi ma dan majalisar dokokin Nijar Alhaji Mamman Sani na Malam Rabi'u, wanda kuma tsohon dan jarida ne, ya ce da ma ba abin mamaki ba ne idan kasarsa ta nemi a warware rikicin cikin ruwan sanyi. "Nijar ba kasa ce mai goyon bayan fitintunu ba ko jayaiya da za ta sa ana ta takun saka da wata kasa makwabciya ba. Wancan nasarar da Niger ta samu a shari'a da aka yi da kasar Benin, gasikya ne ya saya." Fatan sa shi ne wadanda ke nauyin yin shari'ar su yi aiki yadda dokoki suka tanada.

In this Tuesday, May 11, 2010 photo, a nomadic Fulani herder grazes his sheep on parched land around Gadabeji, Niger. At this time of year, the Gadabeji Reserve should be a refuge for the nomadic tribes who travel across the moonscape deserts of Niger to graze their cattle. But the grass is meager, not enough even for the small goats, after a drought killed off the last year's crops. International aid groups once again warn this nation of 15 million on the verge of the Sahara Desert faces a growing food crisis.(ddp images/AP Photo/Sunday Alamba)
Yankin da ake takadama akai na da dimbin arzikiHoto: AP

Burkina Faso ta zargi NIjar ta saba yarjejeniyar da suka cimma tsakaninsu

A yayin da tawagar kasar Burkina Faso ta ke ba da bahasi a kotun duniya, ta zargi hukumomin kasar NIjar da kin mutunta sharuddan da aka rattaba musu hannu akai. Lamarin da minista Bazum ya ce akwai dalili. "Lalle jami'an Nijar sun so su amince da wata yarjejeniya amma daga baya suka ga ba za su yarda da ita ba. Tun lokacin da aka yi wannan aikin Nijar ta aika da kwararun masana kasar Faransa da Senegal suka binciko tarihi da turawan mulkin mallaka suka adana."

epa02847783 President Mahamadou Issoufou of Niger during a meeting with US President Barack Obama and fellow African leaders from Niger, Benin, and Guinea, in the Cabinet Room of the White House, in Washington DC, USA, 29 July 2011. EPA/MARTIN H. SIMON / POOL +++(c) dpa - Bildfunk+++
Shugaba Issoufou ya ce zai yi biyeyya ga hukuncin ICJHoto: picture alliance/dpa

Sai dai kuma Nijar ta amince da shata iyakar ta da Burkina Faso ta bangaren Arewa da can Kudu: Majalisar dokoki kasra ma ta albarkanci wadannan sabbin sharuddan. Babban abin da mutane ke jira a nan shi ne ko talakawan da ke kan iyakar kasashen biyu za su rungumi kaddara.

Mawallafi: Mahaman Kanta
Edita: Mouhamadou Awal