1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Benin da Nijar ta yi rauni

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 13, 2023

Gwamnatin juyin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar, ta sanar da shirinta na dakatar da alakar tsaro da makwabciyarta Jamhuriyar Benin.

https://p.dw.com/p/4WINn
Jamhuriyar Nijar | Yamai | Sojoji | Juyin Mulki | Abdourahamane Tiani | Hulda | Benin
Jagoran gwamnatin juyin mulkin sojan Jamhuriyar Nijar, Janaral Abdourahamane TianiHoto: ORTN/Télé Sahel/AFP

Sojojin juyin mulki na Jamhuriyar Nijar din dai, na zargin makwabciyar tasu Jamhuriyar Benin da bayar damar jibge sojoji da ka iya kai farmaki ga kasarsu karashin jagorancin kungiyar ECOWAs ko CEDEAO. Kungiyar Habaka Tattalin Arzikin Kasashen Afirka ta Yamma wato ECOWAs ko CEDEAO din dai ta ce in har kokarinta na tattaunawar diflomasiyya da sojojin juyin mulkin na Nijar ya ci tura, to a shirye take ta dauki matakin soja a kansu domin mayar da halastacciyar gwamnatin dimukuradiyya karkashin Bazoum Mohammed da sojojin Nijar din suka hambarar.