Tasirin sabon tsarin yakar rashawa
May 19, 2021Kungiyoyin dai sun nunar da cewa sun ji dadin yadda shirin Operation ba Sani ba Sabo da Shugaba Mohamed Bazoum ya kaddamar domin yakar cin-hanci da rashawa, ya fara ritsawa da wani babban jami'i a fadarsa kana dan jam'iyya mai mulki ta PNDS Tarayya wanda ake zargi da karkatar da akalar kimanin miliyan dubu uku na CEFA. Kwanaki kalilan bayan shan ratsuwar kama aiki, Shugaba Bazoum ya yi wa 'yan kasar alkawarin nuna ba sani ba sabo a cikin yaki da matsalar cin-hanci da rashawa, wacce ta dabaibaye kasar shekaru da dama.
Karin Bayani: Bankado badakalar cin hanci a harkar mai a Nijar
Sabon zababben shugaban kasar ta Nijar Mohamed Bazoum ya umurci hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar wato HALCIA da sauran hukumomin yaki da cin hanci na kasar, da su dukufa bincike a ma'aikatar kudi ta kasa da baitul-mali da ma fadarsa, domin zakulo bara gurbin da suka jima suna yi wa tattalin arzikin kasar ta'annati. Fara wannan aiki da wuya, binciken cin-hancin ya rutsa da babban ma'ajin kudi na fadar ta shugaban kasa Malam Ibrahim Amadou Moussa wanda kuma dan jam'iyya mai mulki ne ta PNDS Tarayya, inda ake zarginsa da yin rub da ciki da kudin kasa da suka kai miliyan dubu uku na CEFA. Tuni aka iza keyarsa zuwa gidan maza da ke da tsananin tsaro a garin Say mai nisan kilomita 60 da birnin Yamai.
Kungiyar Transparency International reshen Jamhuriyar ta Nijar ta bakin shugabanta Malam Maman Wada ta bayyana gamsuwarta da wannan mataki. Sai dai Alhaji Idi Abdou da ke zaman tsohon jami a hukumar yaki da cin-hanci da rashawa ta Ligne Verte kana dan fafutuka, ya ce Shugaba Mohamed Bazoum na da kalubale a gabansa wajen iya cimma wannan buri da ya sa a gaba. Sai dai shugaban kungiyar ta Transaparancy International reshen Jamhuriyar Nijar, Malam Maman Wada ya bayyana bukatar ganin Shugaba Mohamed Bazoum ya mika wa kotu takardun badakalar da aka yi bincike shekaru da dama, amma suke boye a fadar shugaban kasa.
Karin Bayani: Yaki da cin hanci tsakanin malaman Nijar
Yanzu haka dai al'ummar Jamhuriyar ta Nijar da dama sun bayyana gamsuwarsu, dangane da yadda sannu a hankali Shugaba Bazoum na daukar matakai da ke zmana tamkar na cinnaka wanda bai san na gida ba a fannin yakar cin-hanci da rashawar. Ko da yake wasu na ganin cewa ba a saurin yabon danyen mai sai an jira rana ta yi an ga yadda ya kasance, domin kuwa gwamnatocin da suka shude a Nijar na kudirar aniyar wanna kokowa ta cin hanci amma daga karshe labarin ya zamo na shafa labarin shuni.