1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Raguwar mutuwar aure a birnin Yamai

Gazali Abdou Tasawa LMJ
January 10, 2023

Babbar kungiyar addinin Muslumci ta Jamhuriyar Nijar wato AIN, ta ce an samu raguwar mace-macen aure a birnin Yamai a shekarar da ta gabata ta 2022 idan aka kwatanta da na shekarun baya.

https://p.dw.com/p/4LyvD
Nijar l Yamai | Aure | Ma'aurata | Mata da Miji
Raguwar mutuwar aure a Jamhuriyar NijarHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

A kowacce shekara babbar kungiyar addinin Muslumci ta Jamhuriyar Nijar din ko AIN a takaice da ke gudanar da shari'a kan rigingimun aure da na gado da sauran matsaloli na zamantakewa, na fitar da rahoto kan yawan mace-macen auren da aka fuskanta a birnin na Yamai. Kungiyar ta AIN ta ce wani abin farin ciki shi ne a shekarar da ta gabata mutuwar auren ta ragu a birnin Yamai, birnin da ya yi kaurin suna wajen mace-macen auren da wasunsu ma ba a wuce mako guda bayan daurawa. Kungiyar taAIN ta ce karairayi da ma'auratan ke yi wa juna ko auren jari da wasu ke yi da kuma rikicin binciken salula, na daga cikin dalilan da ke haddasa mutuwar aure a wannan zamanin. Tuni dai kungiyar SOS Femme et Enfant Victimes de Violance Familiale da ke fafutukar kare hakkin mata da yara a kasar, ta bakin shugabarta Mme Ahmed Mariama Moussa ta bayyana gamsuwarta da wannan ci gaba da aka fara samu a zamantakewar aure a Nijar din. Kungiyar ta AIN dai ta ce akwai dubban aurarrakin da ta ceto a birnin na Yamai a shekarar ta 2022, kuma ta dauki sababbin matakai na ganin adadin auren da ke mutuwa ya ragu a wannan shekara ta 2023 da muka shiga.