1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jagorancin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya

Gazali Abdou Tasawa AMA
September 17, 2020

Jamhuriyar Nijar ta soma jagorancin Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya watannin tara bayan da aka zabi kasar a matsayin daya daga cikin kasashe 10 mambobin masu kujerun wucin gadi

https://p.dw.com/p/3iddb
Mahamadou Issoufou Premierminister von Niger
Hoto: picture alliance/S. Minkoff

A farkon wannan shekara ta 2020 ne aka zabi Nijar tare da wasu kasashe hudu na duniya a jerin kasashe 10 masu kujerar wucin gadi a kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya a wani wa’adi na shekaru biyu. Kuma a farkon wannan wata na Satumba a karon farko a cikin shekaru 40 Nijar din ta karbi shugabancin karba-karba na kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniyar baki daya mukamin da za ta rike har ya zuwa karshen wannan wata. 

An gabatar da taswirori na kasashen duniya dabam-dabam inda sojojin Majalisar Dinkin Duniya suka yi aiki wajen kawo karshen yake-yake da ringingimu da kuma wanzar da zaman lafiya a shekarun baya da kuma ma a halin yanzu, a yayin wani bikin da aka shirya na musamman a albarkacin zagayowar wannan rana.

A jumulce ‘yan Nijar tun daga sojoji zuwa fararan hula sama da dubu 20 suka taba aiki a karkashin hukumomi dabam-dabam na Majalisar Dinkin Duniya tun daga lokacin da kasar ta samun ‘yancin kai zoke yanzu, sanan kuma a karkashin wa’adin shugabancinta na wata daya a kwamitin Sulhu, jamhuriyar Nijar za ta shirya mahawarori kan batutuwa da suka hada da kalubalen shugabancin kasashen duniya wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya bayan kawo karshen annobar covid 19, ko kuma a kan matsalar  hare-haren da ‘yan ta’adda ke kai wa makarantu a wasu kasashe, ko kuma kan yadda lalacewar muhalli da sauran matsalolin tsaro ke yin illa ga rayuwar dan Adam baki daya.