1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanci

Ta'addanci na korar mutane a Nijar

Lateefa Mustapha Ja'afar
July 12, 2023

Kusan mutane 11 sun tsere daga gidajensu cikin wanna wata na Yuli, a yankin Kudu maso Yammacin Jamhuriyar Nijar da ke fama da mayakan jihadi.

https://p.dw.com/p/4Tn31
JAmhuriyar NIjar | Tillaberi | Tsaro | Ta'addanci
Da ma dai al'ummar Tillaberi, sun saba da matsalar hare-haren ta'addanciHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya wato OCHA reshen Yamai ya ce, wadannan mutanen na gudun hijira ne daga tashin hankali da ake alakantawa da mayakan sa-kai a yankin Tillaberi da ke kan iyakar Nijar da Burkina Faso da kuma Mali. Hukumar ta ce fiye da mutane dubu takwas da 430 ne suka fake a garin Ouro Gueladjo, kana kimanin dubu biyu da 140 kusa da Torodi yayin da wasu 215 suka isa Yamai babban birnin kasar. Kaurar dai na da nasaba da harin da aka kai wasu kauyuka guda uku da daren ranar uku ga watan Yulin da muke ciki, inda aka kashe mutane biyu baya ga wa'adin kwanaki uku da maharan suka bai wa mazauna kauyukan da su fice daga gidajensu. Majiyoyin yankin sun ce mutane da yawa na kwana a azuzuwan makaranta.