1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An rasa rayuka a hatsarin kamfanin COMINAK a Nijar

January 17, 2022

Duk da cewa kawo yanzu ba a samu cikakkun bayanin abin da ya hadassa hatsarin ba, amma COMINAK da ke a Arewa maso yammacin Nijar ya ce ya dakatar da ayyukansa har sai an gudanar kammalallen bincike kan lamarin.

https://p.dw.com/p/45cJD
Niger Uranabbau Uran
Hoto: AREVA

Mutane biyu sun halaka a yayin da wasu karin mutum biyun suka ji munanan raunuka a wata rugujewar kayan aiki da ta faru a kamfanin COMINAK da ke sarrafa makamashin nikiliya na Uranium a Jamhuriyar Nijar. 

Hukumomin kamfanin mallakin kasar Faransa ne suka sanar da haka a yammacin ranar Lahadi.