1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Juyin mulki da makomar sojojin Jamus

Bosen Ralf SB/LMJ
August 1, 2023

Juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar Nijar ya zama daya daga cikin koma-baya kan tabbatar da tsaron yankin Sahel na Afirka, inda Jamus take da dakaru da kuma ayyukan raya kasa. Shin lissafi ya kwacewa Jamus ne?

https://p.dw.com/p/4UecC
Jamus | Sojoji | Tsaro | Sahel | Juyin Mulki | Nijar | Makoma
Sojojin Jamus na taka rawa musamman a bangaren bayar da horo a kasashen AfirkaHoto: DW/F. Muvunyi

Duk wani fata da ake da shi a kan Jamhuriyar Nijar, zai zama abin misali kan zaman lafiya a yankin Sahel ya disashe. A shekara ta 2022 da ta gabata kungiyar Tarayyar Turai ta kulla yarjejeniyar shekaru uku kan dangantaka ta fannin soja da kasar da ke yankin yammacin Afirka, wadda ta samu zaman lafiyar siyasa a 'yan shekarun da suka gabata. A watan Mayun wannan shekara majalisar dokokin Jamus ta Bundestag, ta amince da tura sojoji 60 a matsayin masu ba da shawara da taimakon horaswa. Daga filin jirgin saman birnin Yamai, sojojin Jamus suka yi aikin taimakon Rundunar Wanzar da Zaman Lafiya a Mali mai makwabtaka da Jamhuriyar ta Nijar na tsawon shekaru 10. Sai dai ga masanin tsaron yankin Sahel Ulf Laessing na Gidauniyar Konrad Adenauer da ke birnin Bamako na Mali, yana gani an saka buri mai yawa kan Jamhuriyar Nijar wadda ba ta da zaman lafiyar siyasar da ake tunani.

Jamhuriyar Nijar | Yamai | Boris Pistorius | Jamus |  Ziyara
Ministan tsaron Jamus Boris Pistorius yayin ziyararsa a Jamhuriyar NijarHoto: Michael Kappeler/dpa/picture alliance

A watan Afrilun wannan shekara da muke ciki, ministan tsaron Jamus Boris Pistorius da takwararsa ta kula da raya kasashe Svenja Schulze sun kai ziyara zuwa kasashen Mali da Jamhuriyar Nijar. Makasudin ziyarar shi ne batun tsawaita aikin Dakarun Wanzar da Zaman Lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Mali wadanda daga bisani aka kawo katrshen aikin su, abin da ya saka kasashen Turai suka karkata zuwa Jamhuriyar Nijar. A cewar masanin yankin Sahel Ulf Laessinguyin juyin mulkin da sojoji suka yi a Jamhuriyar ta Nijar, ya zo lokacin da lamura suka fara inganta da hadin gwiwa da kasashen duniya. Tun lokacin da Jamhuriyar Nijar ta samu 'yanci daga Turawan mulkin mallaka na Faransa, ta yi ta fuskantar juyin mulki da rashin zaman lafiya na siyasa. Tuni Jamus ta bukaci 'yan kasarta mazauna Jamhuriyar Nijar, kan su saka ido ga sanarwar da take fitarwa.