1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

IS ta dauki alhakin kai hari a Nijar

Gazali Abdou Tasawa AMA
September 18, 2020

Kungiyar IS ta dauki alhakin harin ta‘addancin da aka kai a ranar tara ga watan Agustan da ya gabata a yakin Koure na jamhuriyar Nijar wanda ya yi sanadiyyar halakar Faransawa shida.

https://p.dw.com/p/3ihEG
Niger Französische Touristen getötet
Hoto: AFP

A wani sakon da ta wallafa a shafinta na farfaganfa na Al-Naba a jiya Alhamis, kungiyar ta IS ta yi ikirarin daukar alhakin harin na ranar tara ga watan Agusta 2020 a yankin Koure da ke a kilomita 60 da birnin Yamai, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane takwas da suka hada da ‘yan Nijar biyu da Faransawa guda shida ma’aikatan kungiyar Acted mai zaman kanta ta kasar Faransa. Kuma cibiyoyi da dama da ke bibiyar shafukan farfaganda na kungiyoyin ‘yan ta’adda sun tabbatar da sahihancin sakon da kungiyar ta is ta wallafa.

A sakon nata da ta wallafa kungiyar ta is ta bayyana harin na Koure da sunan walkiya wanda ta ce ya ritsa da Faransa shida da abin da ta kira ‘yan korensu guda biyu ‘yan Nijar.

Kwanaki kalilan dai bayan afkuwar harin ministan cikin gida na Nijar Malam Alkache Alhada ya sanar da cewa sun kama wani mutun daya da ake zargi da hadin bakinsa wajen kitsa harin, ba tare da amma danganta shi da wata kungiya ba. Hukumomin Faransa sun kaddamar da bincike a kan harin na yankin Koure. Kuma tun a ranar 12 ga watan Agusta wani sakamakon farko na bincike ya bayyana cewa an tsara harin ne da nufin takamaimai kashe Turawan yamma. 

Tun dai bayan afkuwar wannan hari, gwamnatin Nijar ta dauki matakin rufe yankin na Koure wanda ga al’ada dubunnan 'yan yawon buda ido daga kasashe dabam-dabam na duniya ke kai ziyara a cikinsa domin kallon garken rakuman dajin da Allah ya arzuta yankin da su.