1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon harin 'yan ta'adda a Nijar

Lateefa Mustapha Ja'afar
November 4, 2021

Sababbin hare-haren ta'addanci a kan iyakokin Burkina Faso da Nijar da Mali, sun yi sanadiyar halaka mutane da dama a Jamhuriyar ta Nijar.

https://p.dw.com/p/42bUN
Symbolild Niger Islamistischer Terrorismus
Hare-haren ta'addanci na yawaita a Jamhuriyar NijarHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

A cewar majiya  daga al'ummar yankin ta bakin wani dan majalisa da ke wakiltar yankin Tillaberi dai, mutane sama da 80 ne aka kashe. Rahotanni sun nunatr da cewa wasua mutanen tara sun yi batan dabo kana wasu 15 suka samu nasarar tserewa a yayin hare-haren da aka kai a ranar Talatar wannan makon. Wata majiya daga yankin ta nunar da cewa, magajin garin na Banibangou na daga cikin wadanda suka rasa rayukansu yayin hare-hare.