1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Gyaran fuska a kan harkokin shari'a

Gazali Abdou Tasawa AH
February 15, 2022

Jamhuriyar Nijar a wani mataki na inganta harkokin shari’a a kasar, gwamnatin ta kafa wani kwamiti na kwararru domin yin gyaran fuska ga wasu manyan kundayen dokokin shari’a.  

https://p.dw.com/p/473aR
Verfassungsgericht in Niamey Niger
Hoto: DW/M. Kanta


Manyan kundayen shari’a guda biyu wadanda Nijar ke aiki da su kawo yanzu, wato kundin hukunci  ko Code Penal da kuma kundin da ke tsara yadda ake tafiyar da shari’a ko Code de procedure penale, kundaye da aka rubuta tun na lokacin samun ‘yancin kan kasar shekaru kusan 60 da suka gabata. Kuma mafi yawancin kudire-kudiren da suka kunsa kwaikwayo ne aka yo daga Turawan mulkin mallaka na Kasar Faransa wanda sannu a hankali mahukuntan kasar ta Nijar suka fahimci cewa sun tashi aiki ta la’akari da yadda ba sa taimaka wa ga warware wasu matsalolin shari’a na wannan zamani a kasar. Mai shari’a Maman Sani Ousseini Djibaje shugaban kwamitin kwararru ya zano wasu daga cikin matsalolin da suka sanya gwamnati ta dauki wannan mataki na yin gyara:

Daidaita harkokin shari'ar Nijar daidai da al'adun jama'ar kasar
 ''Misali in ka dauki fannin gidan kaso a yau a Nijar, muna da 'yan kaso wajen dubu goma da 900 da wani abu. Cikin su wajen dubu shida ba a yi masu shari’a ba. Kenan wadanda ba a yi wa shari’a ba  sun fi wadanda aka yi wa yawa. Matsalar kuma daga dokar ce, domin da an kamo mutum an kawo shi a gaban alkali, tun da doka ta ce in ka yi laifi a kai ka gidan kaso. To alkali sai ya kama mutun ya kai ya aje gidan kaso har sai lokacin da aka yi maka shari’a. Wannan wa’adin da mutum zai zauna kaso yana jiran shari’a muka gani ya yi tsawo. Ya kamata a rage shi dangance da girman laifin da mutum ya yi.'' Mai shari’a Maman Sani ya ce Wata Matsalar ta daban wacce ta sa gwamnatin daukar wannan mataki na kwaskware kundayen shari’a na kasar ita ce ta’addanci : '' Lokacin da ta’addanci ya shigo mana cikin kasa wajen shekara ta 2015, akwai dokoki da aka dauka. To wadannan dokoki suna cike da rauni, suna bukatar gyara. A san mine ne ma’anar dan ta’adda. Wani hukunci za a iya yi masa. Yaya ya kamata a yi masa shari’a ''

Samun ingantacciyar shari'a a tsakanin al'umma talaka da mai kudi ba tare da nuna bambamci ba.
Kwamitin gyaran huska ga dokokin shari’ar kasar ta Nijar ya kunshi mambobi 31 da suka hada da masana ilimin doka da kuma ‘yan farar hula. kuma Malam Boubacar Lawal wakilin kungiyar RODAHD a cikin kwamiti ya bayyana abin da ke ci masu tuwo a kwarya da za su nemi shawo kansa a wannan zama : ''Lallai mu ba masana ba ne na musamman bisa kan shari’a. Amma a yau ‘yan kasa muna ganin kamar ana ma wasu shari’a ta gaskiya, wasu kuma ba a yi masu ita, ‘yan kasa ba su zamo daya ba a idon shari’a. to wannan matsala ce za mu yi kokari a wannan kwamiti, a dauki mataki ta yadda ‘yan kasa za su zamo daya a wajen shari’a.''

Bude layin waya ga jama'a domin su ba da shawarwari ga masana kwamitin da ke yin sauye-sauyen shari'ar
 A baya dais au 18 Nijar na yin gyaran fuska ga wasu kudire-kudire da kundayen suka kunsa. Amma wannan shi ne karo na farko da za a yi wa kundin baki daya wanka. Yanzu haka dai kwamitin na gyaran kundayen shari’a a Nijar ya tanadi lambar waya ta musamman wato 115 wacce illahirin ‘yan kasa daga ko ‘ina za su iya kirowa a kyauta su bayar da shawarwari kan sauye-sauyen da suke son ganin an aiwatar da su a sabon kundin shari’ar kasar ta Nijar da zummar inganta harkokin shari’a a kasar .