1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Dambarwa kan jadawalin zabe

Abdoulaye Mamane Amadou
May 31, 2018

Hukumar zabe mai zaman kanta ta (CENI) ce ta yaye wa jam'iyyun siyasar Nijar jadawalin manyan zabukan dake tafe da hukumar ta bayyana za a soma a farkon shekarar 2020.

https://p.dw.com/p/2yiQi
Demokratischen Republik Kongo | Wahlkommision |  Wahlschein
Hoto: DW/F. Quenum

A yayin wata ganawa ta musamman da jam'iyyun siyasar kasar da kungiyoyin farar hula da 'yan jarida, hukumar zaben mai zaman kanta ta bayyana jadawalin da ta ke shirin kaddamarwa na zabubukan gama gari da suka hada da zaben kananan hukumomi na jihohi da yankuna da ma zabubukan 'yan majalisun dokoki da na shugaban kasa zagayen farko wanda hukumar ta ce tana cikin shirye shiryen, domin ganin ta gudanar da zabubukan a cikin koshin lafiya,