1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Halitta da Muhalli

Matakan kare rakuman daji a Nijar

Gazali Abdou Tasawa
November 22, 2018

Gwamnatin kasar Nijar ta sanar da soma gwajin kafa wani sabon garken rakuman daji na yankin Koure na Kudu maso Yammacin kasar zuwa fadamar yankin Gadabedji a cikin jihar Maradi. 

https://p.dw.com/p/38hBF
Niger Giraffen aus dem Kouré Giraffe Reserve
Hoto: Getty Images/AFP/B. Hama

A wani taron manema labarai da ya kira a jiya Laraba ministan muhalli na kasar ta Nijar Malam Almoustapha Garba ya ce sun dauki matakin ne domin kare lafiyar rakuman dajin na Koure wadanda ke zama garken karshe na nau'in irin wannan rakumin daji a duniya baki daya. 

Ministan ya ce rakuman dajin wadanda guda 50 ne a shekara ta 1996 a fadamar ta koure, a yanzu sun kai 612 a yankin wanda sannu a hankali ke zama hadari ga rayuwar dabbobin a sakmakon yawansu da kuma yawan hadurran mota da mamayar hamada da sarar dajin da manoma ke yi don samun filin noma. 

Matakin kwashe wasu rakuman dajin na Koure zuwa Gadabedji inda da ma rakuman suka yi rayuwa a shekarun baya zai shafi a tashin farko rakuman 10 maza uku.