1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Nijar ta rage kudin zuwa aikin Hajjin bana

Mahaman Kanta RGB
April 5, 2023

Hukumomin kasar Jamhuriyar Nijar sun sanar da rage kudin zuwa aikin Hajji a wani kokarin bai wa al'ummar Musulmin kasar damar zuwa kasa mai tsarki.

https://p.dw.com/p/4PhBj
Birnin Makka ya yi cikar kwari
Birnin Makka ya yi cikar kwariHoto: Amr Nabil/AP/picture alliance

A yammacin ranar Litinin da ta gabata, aka gudanar da taron da ya hada kan Ministan Kasuwanci da shugaban Hukumar Kula da Hajji da Umrah wato COHO da wakilan kamfanonin jigilar maniyata a birnin Yamai, in da aka fitar da sanarwar rage kudin zuwa aikin Hajjin.

Hukumomin sun sanar da rage kudin daga CFA 3,603,840 zuwa 3,225,8733 wanda ke nuni da cewa, an sami ragi na CFA 325,107. Daga bisani aka baiyana sunayen kamfanonin jiragen saman da aka bai wa kwangilar jigilan maniyatan zuwa kasar Saudiyya.

Sai dai ana ganin tsugune ba ta kare ba duk da wannan matakin na yin sassauci, a sakamakon sabbin ka'idojin da aka gindaya na kafa rukuni, wanda sai kamfani ya kawo shedar zuba kudi na kimanin CFA 2,000 000 da kuma rijistan maniyata 1,000 kafin samun izinin kafa rukunin ko kuma Group. A ranar 14 ga wannan watan na Afrilu za a rufe karbar rijistan maniyata a kasar Jamhuriyar ta Nijar.