1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Niger: Koyar da yara darusan zaman duniya ta tatsuniya

February 4, 2020

A jihar Maradi da ke jamhuriyar Nijar, tatsuniya ce wani 'dan asalin jihar mai suna Sani Buda ya ke anfani da ita wurin ilimatar da yara da nishandantar da su darusan zaman duniya.

https://p.dw.com/p/3XFeg
Yara cikin nishadi a jihar Maradi
Yara cikin nishadi a jihar MaradiHoto: A. Abdou

Sani Buda dai wani dan asalin jahar Maradi ne, wanda ya shahara kuma ya kware wurin nishadantar da yara kanana ta hanyar gatana, wato tatsuniya. Yara da yawa ke zuwa sauraron tatsuniyoyin nashi a wani gidan gatana da ya bude, bugu da kari makarantun boko da dama da gidajen karatu da raya al’adu na gayyatar shi, domin ya yi wa dalibansu gatana ko tatsuniya, dan nishadantar da su. Ya kan yi amfani ne da kida da rawa da kuma busa irin na gargajiyar, Nijar da Afirka kuma yana anfani da darusa na gatana domin ilimantar da yara yadda ake zaman duniya. Sani Buda ya koyo iya tatsuniya ne a hannun kakarshi wadda ta yi rainonshi, shi mutum ne mai matukar son da'da'da wa yara kamar yadda ya ke fadi.Dimbin yara ne ke zuwa sauraron tatsuniyarshi, wasu a gidan gatana da ya bude, wasu a BPI, wasu kuma a AFRAMI, har a harabar Alliances francaise yakan je ya yi wa yara gatana. Wakilin DW Hausa jihar Maradi, ya samu yi wa yaran tambayoyi bayan kammala aji na farko na tatsuniyar, inda ya tambayi yaran ko mi yasa suke sha’awar gatana, musaman ta Sani Buda, ga abunda wasunsu suka bayana.

Yara 'yan makaranta a aji, a jamhuriyar Njiar
Yara 'yan makaranta a aji, a jamhuriyar NjiarHoto: DW/J. Henrichmann/F. Quenum


''Muna samun nishadantuwa kuma muna koyon azanci, da iya zaman duniya tare da daina yin karya ga iyaye a gida. Gaskiya muna koyon abubuwa sosai daga gatanar da ya ke yi mana''.


Wannan gatana da yake yi tsahon shekaru da dama, ta kai shi kasashe da dama na Afrka da Turai kuma ta bashi lambobin yabo kamar yadda ya bayyana DW. So da yawa makarantun boko, da kungiyoyin kasa da kasa irin su UNICEF kan gayyaci Sani Buda domin yi wa yara gatana da zummar basu darausan rayuwa kamar yadda mai yin gatanar ya bayana. To ko yaya ake kallon gudumuwar wannan bawan Allah a ma’aikatar raya al'adu ta jihar Maradi? Shugaban wannan ma’aikata malam Usamane Musa ya bada sheda kuma ya ce sun yaba da kokarinsa saboda ya fidda sunan Nijar zuwa kasashen waje ta hanyar gatanar da yake yi hade da kide-kide domin karawa abin armashi a wajen yara dan a ganinsa ta haka ne abin zai fi shiga ransu tare da maidaa hankalin wajen koyan darusan zaman duniya.