1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Netherlands: An kama dubban masu kare muhalli

September 10, 2023

A karshen wannan makon ne jami'an 'yan sanda a Netherlands suka kama dubban masu rajin kare muhalli bisa zarginsu da rufe manyan hanyoyin kasar na kwanaki biyu a jere.

https://p.dw.com/p/4WAhi
'Yan sanda sun fesa ruwa domin tarwatsa masu rajin kare muhalli da ke zanga-zanga a Netherlands
Hoto: Mouneb Taim/AA/picture alliance

Magajin garin Hague ya ce, jami'an sandan sun kama mutane kimanin 2,500. A kalla masu fafatukar 10,000 ne suka rufe babbar hanyan da ke zuwa birnin Hague na tsawon sa'oi a ranar Asabar. Ko a ranar Lahadin ma, jami'an 'yan sanda sun tarwatsa masu zanga-zangar bisa zargin rashin yinta a babban tashar birnin kamar yadda aka ba su damar yi tun da fari.

Masu rajin kare muhallin dai na zanga-zanga ne domin nuna adawa da matakin gwamnatin kasar na bada tallafi ga kamfanonin da ke samar da makamashin da ke fitar da hayaki mai gurbata muhalli kamar yadda suka yi watannin baya-bayan nan.

Gwamnatin Netherlands dai ta ware tallafin fiye da dala milliyan 40 a kowace shekara ga kamfanonin, sai dai masu fafutukar na cewa, ba za su daina adawa da hakan ba har sai gwamnati ta daina tallafawa kamfanonin mai da iskar gas da kudin al'umma.