Nepal: Girgizar kasa ta kashe mutane sama da 3000
April 27, 2015Talla
Mukaddashin sufeto janar na rundunar 'yan sanda kasar Komal Singh Bam ya ce bisa alkaluman da suka samu yanzu haka mutane dubu uku da dari biyu da sha takwas ne suka rasu a Nepal din baya ga 60 a kasar Indiya da kuma wasu 20 a yankin Tibet.
Masu aikin ceto suka ce dubban mutane musamman ma wanda ke yankunan karkara na cikin mawuyacin hali saboda gaza kaiwa garesu don basu agaji sakamakon lalacewar hanyoyi.
Kasashen duniya da suka hada Amirka na ta kokari wajen kai kayan agaji da nufin tallafawa wanda wannan Ibtila'i na girgizar kasa mai karfi maki 7.8 a ma'aunin Richter ya shafa kasar ta Nepal da wasu kasashen da ke makota da ita ko da dai ta'adin ya fi yawa a Nepal din.