Taron warware rikicin Gabas ta Tsakiya
January 15, 2017Jami'an diplomasiya daga kasashe fiye da 70 na duniya sun hallara a birnin Paris na kasar Faransa, domin lalubo hanoyin samar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya tsakanin Palesdinawa da Yahudawa. Yayin bude taron Shugaba Francois Hollande na Faransa ya yi gargadi kan hadrin da ke cikin watsi da shirin samar da zaman lafiya taksanin sassan biyu.
Sai dai yayin da Palesdinawa suka yi maraba da shirin, tuni gwamnatin Isra'ila karkashin Benjamin Netanyahu ta yi watsi da matakin wanda ta ce akwai lauje cikin nadi. Haka na zuwa yayin da ranar Jumma'a mai zuwa sabon Shugaban Amirka Donald Trump zai dauki madafun iko, wanda kuma ya ce neman hanyoyin sasanta bangarorin na cikin abubuwan da zai saka a gaba. Sai dai akwai shakku kan shirin sabuwar gwamnatin ta Amirka, saboda irin kalaman da suke fitowa daga bakin Trump tun kafin ya dare karagar mulki.