1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

140911 Italien China

September 14, 2011

Ƙasar Italiya wadda bashi yawa katutu ta duƙufa wajen neman taimako daga ƙasar China domin magance matsalolin da yanzu ke barazanar zama ruwan dare a tsakanin wasu ƙasashen Turai.

https://p.dw.com/p/12ZIA
Matsalar kuɗi a Turai na ƙara bazuwa zuwa ƙasashe kamar ItaliyaHoto: picture alliance/dpa

A halin da ake ciki ma'aikatar kuɗi a birnin Rom ta tabbatar da wata ganawa da ta gudana tsakanin ministan kuɗin Italiya Giulio Tremonti da shugaban asusun ba da tallafi mafi girma a China, Lou Jiwei. Bisa wani rahoto na jaridar Financial Times, tattaunawar ta mayar da hankali ne musamman kan sayen wasu hannyen jari na gwamnatin Italiya.

A 'yan kwanakin nan dai ƙasar Italiya ta zama tamkar wata rijiya ce da zurfinta ba shi da iyaka. A makonni baya bayan nan babban bankin Turai ya saye hannayen jarin ƙasar ta Italiya da kuɗin su ya kama dubban miliyoyi na Euro. To sai dai ba ta canza zane ba, domin har yanzu ba bu mai sha'awar zuba jari a ƙasar, duk da ƙarin kuɗin ruwa na kashi 5.6 cikin 100 wato mafi yawa tun bayan fara amfani da takardun kuɗin Euro.

Yanzu haka dai Italiya ta waiwayi ƙasar China game da matsalar ta bashi. A makon da ya gabata ministan kuɗin Italiya Giulio Tremonti ya gana da Lou Jiwei, shugaban asusun zuba jari na gwamnatin China. Giuliano Noci masanin harkokin ƙasar China a jami'ar birnin Milan ya ce ana ƙirga abubuwan da tattaunawa ta ƙunsa da yatsar hannu.

"A yanzu China ce ta fi yawan kuɗaɗe a hannu da suka kai dala miliyan dubu har sau dubu uku da ɗari biyu. Waɗannan kuɗaɗe masu yawan gaske wanda ya ninka jimilar kayan da ake samarwa cikin gida har sau biyu. Haƙiƙa China na da sha'awar nahiyar Turai da ma Italiya, amma ta fi mayar da hankali kan ainihin buƙatunta."

Berlusconi Tremonti Italien Rom Finanzkrise
Silvio Berlusconi, a dama, da ministan kuɗi Giulio TremontiHoto: AP

Da wata manufa ta daban China ke son taimakawa

Abin nufi dai shine China ba za ta zama tamkar wata kyakkyawar mai ceto daga gabas mai nisa ba wajen zuba jari a cikin kadarorin gwamnatin Italiya. Irin wannan fata da aka nuna game da rikicin basussukan ƙasashen Girika da Portugal ya bar baya da ƙura. Masana sun nuna cewa China na da niyar zuba jari a masana'antu daban daban na Italiya da suka haɗa da fannonin fasaha, makamashi, waɗanda mafi yawa mallakin gwamnati ne. Shigar da China a waɗannan fannoni masu riba na nufin ƙarin kuɗin shiga a baitul malin gwamnati, inji Giuliano Noci.

"Ko shakka babu China na da sha'awar masana'antunmu masu muhimmanci, baya ga haka tana da sha'awar samun goyon baya a fagen siyasa na ƙasa da ƙasa. A saboda haka tana iya sayen wani kaso na hannayen jarin gwamnatinmu sannan za ta so Italiya ta saka mata wajen goya mata baya a fagen siyasar duniya."

Kwantar da hankulan ƙasashen Turai bayan an waiwayi China

Italien Euro Demonstration in Rom gegen Sparhaushalt
Al'umar Italiya na yawaita zanga-zangar nuna adawa da matakan tsimi na gwamnatiHoto: picture-alliance/dpa

Wannan tamkar wani ciniki ne ba ni gishiri in ba ka manda. Ba da daɗewa ba ne dai ministan kuɗin Italiya Tremonti da Firaminista Berlusconi suka yi kira da a samar da wata kariya ga kasuwannin cikin gida daga kayakin dake fitowa daga China. Amma yanzu Tremonti ya juya wa Turai baya yana neman China da ta zuba jari a ƙasarsa. Shi kuma Berlusconi zai yi tattaki zuwa birnin Brussels domin kwantar da hankulan ƙawayensa na Turai. A wani mataki na yin gaba kai, Berlusconi ya soki lamirin 'yan adawa na cikin gida kana ya jaddada cewa Italiya ba ta da matsalar bashi.

"Kamfanoni masu zaman kansu da iyalai da bankuna suna da isassun kaɗaɗe. Magidanta a Itaiya sun tara kuɗaɗe masu yawa. Idan aka kwatanta bashin dake kan ƙasa da kadarorin kamfanonin Italiya da na Iyalai za a ga cewa muna bayan Jamus da mataki ɗaya musamman game da abin da ya shafi wadata."

Yayin da firaministan ke ƙoƙarin mayar da matsalar bashin tamkar ba ta da yawa, wakilan gwamnatin a birnin Rom sun sanar da ɗauƙar sabbin matakan tsimi da tanadi.

A wannan Larabar majalisar dokokin ƙasar ta albarkaci shirin tsuke bakin aljihu na ƙarshe, wanda hakan ke zama wata nasara ga Berlusconi ga abin da ya kira ƙuri'ar amincewa da gwamnatinsa.

Mawallafa: Tilmann Kleinjung/Mohammad Nasiru Awal
Edita: Umaru Aliyu