1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar hawa kan teburin sulhu a rikicin kasar Yemen

Gazali Abdou Tasawa/LMJApril 27, 2015

Amirka ta ce al'ummar kasar Yemen ne ya kamata su samarwa da kansu mafita bawai wasu kasashe daga waje ba.

https://p.dw.com/p/1FFrX
Hare-haren Saudiya a Yemen
Hare-haren Saudiya a YemenHoto: Reuters/Str

Sakataren harkokin waje na Amirka John Kerry ne ya bayyana hakan inda ya bukaci dukkan bangarorin da ke cikin rikicin na Yemen da su sassauta tashe-tashen hankula tare da zama kan teburin sulhu. Kerry ya kara da cewa yana tsammanin za su tattauna batun rikicin na Yemen da takwaransa na kasar Iran Mohammad Javad Zarif a tattaunawar da za su yi nan gaba kadan. Mutane da dama ne dai suka rasa rayukansu yayin da wasu dubbai suka kauracewa gidajensu tun bayan da kasar Saudiya ta kaddamar da hare-hare a kasar ta Yemen sama da tsahon makwannin ukun da suka gabata.