1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taro domin kawo karshen rikicin Yemen

Lateefa Mustapha Ja'afar
September 5, 2018

Jakadan musamman na Majalaisar Dinkin Duniya a Yemen, Martin Griffiths ya bayyana fatan samun mafita a taron da za su gudanar tsakanin bangarorin da ke yakar juna a Yemen din, domin shawo kan rikicin kasar.

https://p.dw.com/p/34NXi
Jemen Beerdigung von Opfern eines Luftangriffs in Saada
Rikicin Yemen na ci gaba da lakume rayukaHoto: Reuters/N. Rahma

Griffiths ya bayyana hakan ne kwana guda gabanin taron da za su gudanar a birnin Geneva wanda Majalisar Dinkin Duniya ta shirya, inda ya ce al'ummar kasar sun gaji da yakin da suke fama da shi na tsahon shekaru. Mutane da dama ne da suka hadar da fararen hula har ma da kananan yara suka hallaka sakamakon ruwan bama-banman da Saudiyya da kawayenta ke yi a kasar karkashin rundunar taron dangin da take wa jagoranci, a wani mataki da Saudiyyan ta ce na kare halastacciyar gwamnatin kasar ne.