1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Naɗa sabon shugaban IMF

May 18, 2011

Amirka ta miƙa buƙatar naɗa sabon shugaban IMF har sai an gama shari'ar da ake wa Dominique Strauus-Kahn, shugaban asusun mai ci yanzu.

https://p.dw.com/p/11Izx
Dominique Strauss-Kahn, a lokacin da ake shirin sauraron shari'arsaHoto: AP

Ƙasar Amirka ta yi kira ga shugaban asusun ba da lamuni na duniya IMf, Dominique Strauss-Kahn da ya sauka daga wannan muƙami nasa. Sakataren kuɗin Amirka, Timothy Geitner ya ce akwai buƙatar gaggauta naɗa sabon shugaban asusun na riƙon ƙwarya har sai an tattance shari'ar da ake wa Strauss-Kahn. An ki bashi beli a 16 ga wannan wata ne bisa zargin da ake masa na cewa ya yi yuƙunrin yi wa wata mace fyaɗe. To amma ya musunta wannan zargi da wata ma'aikaciyar otel ta shigar yana mai cewa shi da ita basu gana ba. A ƙasar Faransa da yawa daga cikin shugabannin jam'iyyar Socialist da Stauss-Kahn ke jagoranta sun bayyanar da fushinsu game da yadda aka ta gabatar da shi a gaban 'yan jarida bayan da aka kama shi. A dai halin da ake ciki yanzu kafafen yaɗa labarun birnin New York sun ce ana sa ido akan Strauss Kahn a kurkukun da ake tsare da shi a wani tsibiri domin tsoron cewa mai yiwuwa ne ya halaka kansa da kansa.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu