1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An tabbatar da sa wa Navalny guba

Abdul-raheem Hassan MNA
October 7, 2020

Babban dan hamayya a kasar Rasha Alexy Navalny ya zargi tsohon shugaban gwamnatin Jamus Gerhard Schroeder da karbar kudi daga Shugaba Vladimir Putin domin kare shi daga zargin kisan kai.

https://p.dw.com/p/3jXXr
Alexej Nawalny
Hoto: YouTube - vDud/Reuters

Da yake hira da jaridar Bild da ake bugawa a Jamus, Navalny ya ce abin takaici ne Gerhard Schroeder ya nemi karyata yunkurin halaka shi ta hanyar sa masa guba.

Gwamnatin Jamus na shirin daukar mataki na gaba, bayan da hukumar sa ido kan amfani da guba ta duniya ta tabbatar da kaiwa madugun adawar na Rasha hari da guba.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kotu ke fara shgari'ar wani dan bindigan da ya kashe tsohon kwamandan Checheniya a Jamus. Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce gwamnatin Rasha za ta dandana kudarta idan ya tabbata tana da hannu a kisan.