1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Corona ta sake bayyana a China

Abdourahamane Hassane
August 2, 2021

Annobar corona nau'in delta ya bazu a China, kusan shekara guda bayan da kasar ta kawar da covid 19 a shekara ta 2020.

https://p.dw.com/p/3yRdA
China Wuhan Krankenhaus Coronavirus
Hoto: Xinhua News Agency/picture alliance

Yanzu haka an saka dubban jama'a cikin hali na kulle, a yankunan dabam-dabam na kasar ta China sakamakon sake bazuwar annobar. Hukumomin kiwon lafiya sun ce kawa yanzu mutane 300 suka kamu da cutar coronar nau'in delta har a Wuhan inda corona ta fara bulla da kuma tsibirin Hainan da ke a yankin kudanci na kasar.